Shugabannin Kasashen Yammacin Afrika Sun Jaddada Daukan Matakin Yaki Da Ta'addanci
(last modified Tue, 06 Mar 2018 12:01:07 GMT )
Mar 06, 2018 12:01 UTC
  • Shugabannin Kasashen Yammacin Afrika Sun Jaddada Daukan Matakin Yaki Da Ta'addanci

Shugabannin kasashen yammacin Afrika sun jaddada aniyarsu ta hadin gwiwa a tsakaninsu a fagen yaki da ta'addanci.

A zaman taron shugabannin kasashen yammacin Afrika a birnin Ouagadougou fadar mulkin kasar Burkina Faso sun yi tofin Allah tsine kan harin ta'addancin da aka kai birnin na Oaugadougou tare da jaddada niyarsu ta hadin gwiwa a fagen kalubalantar duk wani aikin ta'addanci a kasashensu.

A ranar Juma'ar da ta gabata ce wasu gungun 'yan ta'adda suka kaddamar da hare-haren ta'addanci kan ofishin jakadancin Faransa da ke birnin Ouagadougou da kuma wata cibiyar rundunar sojin kasar, inda suka kashe mutane akalla takwas, kuma wasu gungun 'yan ta'adda daga kasar Mali sun bayyana cewa suke da alhakin kai harin na Burkina Faso.