Mutane 110 Zazzabin Lassa Ya Kashe A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28873-mutane_110_zazzabin_lassa_ya_kashe_a_najeriya
Hukumomin kiwan lafiya a Najeriya, sun ce mutane 110 ne cutar zazzabin lassa ta yi ajalinsu cikin 353 da suka kamu da ita tun daga farkon wannan shekara ta 2018.
(last modified 2018-08-22T07:01:31+00:00 )
Mar 07, 2018 02:17 UTC
  • Mutane 110 Zazzabin Lassa Ya Kashe A Najeriya

Hukumomin kiwan lafiya a Najeriya, sun ce mutane 110 ne cutar zazzabin lassa ta yi ajalinsu cikin 353 da suka kamu da ita tun daga farkon wannan shekara ta 2018.

A cikin makon jiye ne hukumar lafiya ta duniya WHO, ta sanar da mutuwar mutane 72 cikin 317 da aka tabbatar sun kamu.

Cibiyar takaita yaduwar cutuka ta Najeriiya (NCDC), ta ce an samu bullar zazzabin a jihohin kasar 18 a cikin 36.

Kwayar cutar na yaduwa ne ta hanyar tu'ammali da abinci da kuma kayayyakin amfanin gida da suka gurbata da fitsari da kashin bera, haka zalika kuma tana yaduwa daga mutum zuwa mutum ta hanyar ta shafar duk wani irin ruwa daga jikin mutumin da ya kamu.

Cutar wacce ta samo asali daga wani gari da ake kira Lassa a jihar Borno, dake arewa maso gabashin Najeriya a shekara 1969, na da kamanceceniya da cutar Ebola.