Sakataren Harakokin Wajen Amurka Ya Fara Ziyarar Aiki A Afirka
Sakataren harakokin wajen Amurka ya fara ziyarar aiki a wasu kasashen Afirka inda ya fara da kasar Ethiopia a jiya Talata.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa a jiya talata sakataren harakokn wajen Amurka Rex Tillerson ya fara ziyarar aiki a wasu kasashen Afirka da suka hada da Najeriya, da Habasha, da Somaliya, da Sudan Ta Kudu da kuma kasashen da ke yankin Tabkin Chadi duk dai kasashen da suka yi fama da irin wadanan matsaloli na tsawon lokaci.
Sakataren Harkokin wajen Amurka ya bayyana cewa kasarsa za ta taimakawa wadannan kasashen domin kalubalantar yan ta'adda da masu tsattsauran ra'ayi.
Cikin jawabin da ya gabatar kafin tashinsa daga kasar Amurka, Rex tillerson ya tabbatar da mahimancin kasashen Afirka game manufofin Amurka.
Wannan ziyarar dai na zuwa ne makwanni kadan bayan kalamman cin mutuncin da shugaban Amurkar, Donald Trump ya yi wa wasu kasashen Nahiyar.