Sakataren Harkokin Wajen Amurka Ya Gana Da Shugaban Kungiyar Tarayyar Afrika
(last modified Thu, 08 Mar 2018 19:01:29 GMT )
Mar 08, 2018 19:01 UTC
  • Sakataren Harkokin Wajen Amurka Ya Gana Da Shugaban Kungiyar Tarayyar Afrika

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka ya bayyana shirin gwamnatin kasarsa na taimakawa kungiyar tarayyar Afrika a fagen yaki da ta'addanci.

A ganawarsa da shugaban kungiyar tarayyar Afrika Moussa Faki Mahamat a cibiyar kungiyar ta AU da ke birnin Addis Ababa na kasar Habasha a yau Alhamis: Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Rex Tillerson ya bayyana shirin Amurka na gudanar da ayyukan hadin gwiwa tsakaninta da kungiyar tarayyar Afrika a fagen tsaro da yaki da ta'addanci, kasuwanci, gudanar da ayyukan raya kasa, yaki da cin hanci da rashawa da kuma matsalolin tashe-tashen hankula da suke ci gaba da addabar nahiyar Afrika. 

Dangane da kalaman batanci da cin zarafi da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi kan kasashen nahiyar Afrika a watan Janairun wannan shekara; Shugaban kungiyar tarayyar Afrika Faki Mahamat ya ce ya samu sakon wasika daga Trump kuma har ya aike da ita ga shugabannin Afrika, don haka wannan matsala ta zame labari kuma an rufe shafinta.   

Tun a ranar Talatar da ta gabata ce Rex Tillerson ya fara gudanar da ziyarar aiki a nahiyar Afrika, inda zai ziyarci kasashen Habasha, Kenya, Djibouti, Chadi da Nigeriya.