Kotun ICC Ta Yanke Hukunci A Kan Tsohon Madugun 'Yan Tawayen Congo
Mar 09, 2018 01:28 UTC
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta yanke hukunci a kan tsohon madugun 'yan tawayen Congo Germain Katanga, wanda aka same shi da hannu wajen cin zarafin jama'a da aikata laifukan yaki.
Germain Katanga wanda ya jagoranci mayakan 'yan tawaye a Congo, kotun ta same shi da laifin jagorantar hare-hare a kan kauyuka da cin zarafin jama'a da kone gidajen fararen hula da wawushe kaddarorinsu.
Baya ga daurin shekaru 12 a gidan kaso, Germain Katanga zai biya kudade da suka kai kimanin dalar Amurka miliyan 1 a matsayin diyya ga jama'ar da ya yi sanadiyyar lalata kaddarorinsu.
Tags