Ziyarar Ministan Harakokin Rasha A Habasha
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28923-ziyarar_ministan_harakokin_rasha_a_habasha
Ministan harakokin wajen kasar Rasha ya kai ziyara zuwa kasar Ethiopia
(last modified 2018-08-22T07:01:32+00:00 )
Mar 09, 2018 08:15 UTC
  • Ziyarar Ministan Harakokin Rasha A Habasha

Ministan harakokin wajen kasar Rasha ya kai ziyara zuwa kasar Ethiopia

A jiya alhamis ne ministan harakokin wajen kasar Rasha ya shiga birnin Adis ababa na kasar Habasha, inda ake sa ran a wannan juma'a zai gana da Hailemariam Desalegn piraministan ficin gadi na kasar da Workneh Gebeyehu ministan harakokin wajen kasar

Ministan harakokin wajen Ethiopia ya bayyana cewa wannan ziyara da takwaransa na kasar Rasha ya kai kasar za ta kara donkon zuminci da kuma bunkasa tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu.

Ana sa ran a wannan juma'a ce ministocin biyu za su tattauna kan yadda aka kara bunkasa alaka tsakanin kasashen biyu a bangaren ilimi, kiyon lafiya, Noma da sauransu.

A ranar Litinin din da ta gabata ce ministan harakokin wajen Rasha ya fara ziyara a kasashen Afirka, inda ya zuwa yanzu ya ziyarci kasashen Angola, Namibiya, Mozambic da Zimbabwe.