Gwamnatin Burkina Faso Ta Zargin Jami'an Tsohuwar Gwamnatin Kasar Da Ta'addanci
(last modified Sat, 10 Mar 2018 05:23:10 GMT )
Mar 10, 2018 05:23 UTC
  • Gwamnatin Burkina Faso Ta Zargin Jami'an Tsohuwar Gwamnatin Kasar Da Ta'addanci

Gwamnatin kasar Burkina Faso ta zargi wasu jami'an tsohuwar gwamnatin kasar ta tsohon shugaba Blaise Compaoré da hannu cikin hare-haren ta'addancin da kasar ta fuskanta.

Tashar talabijin din France 24 na kasar Faransa ya ba da rahoton cewa ministan tsaron cikin gidan kasar Burkina Fason Clement Savadogo yana fadin cewa gwamnatin kasar ta gano cewa wasu manyan jami'an tsohuwar gwamnatin Blaise Compaoré da aka hambarar a kasar suna da hannu cikin ayyukan ta'addancin da ke faruwa a kasar.

Mr. Savadogo ya kara da cewa gwamnatin shugaba Roch Marc Christian Kaboré ta kasar za ta ci gaba da karin bayani dangane da wannan lamari sannan kuma za ta dau matakan da suka dace kansa.

Cikin 'yan watannin bayan nan kasar Burkina Fason ta fuskanci hare-haren ta'addanci, na baya-bayan nan shi ne harin da aka kai ranar Juma'a, 2 ga watan Maris din da ta gabata a helkwatar sojin kasar da ofishin jakadancin Faransan da ke birnin Ouagadogou, babban birnin kasar da yayi sanadiyyar mutuwar wani adadi mai yawa na mutan.