Najeriya: An kashe Mutane 10 A grin Daffo Da Ke Jahar Plateau
Mar 10, 2018 15:31 UTC
Kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya ambato majiyar tsaro na cewa wadanda aka kashe din sun kunshi mata biyar da karamin yaro guda sai maza hudu.
Bugu da kari maharan sun barnata dukiya a cikin garin da suka kai wa hari, sannan su ka yi batan dabo.
Jami'an tsaro sun sanar da baza komarsu domin kamo maharan.
A cikin watannin bayan nan an tsananta kai hare-hare a yankunan da suke tsakiyar kasar bisa dalilai na kabilanci. Daruruwan mutane ne dai su ka rasa rayukansu a cikin watanni kadan.
Wadannan irin hare-haren dai suna afkuwa ne a daidai lokacin da kungiyar Boko Haram take tsananta kai hare-hare a yankin arewa maso gabacin kasar.
Tags