Senegal: An Hana 'Yan Adawa Yin Gangami Akan Demokradiyya
(last modified Sat, 10 Mar 2018 19:03:04 GMT )
Mar 10, 2018 19:03 UTC
  • Senegal: An Hana 'Yan Adawa Yin Gangami Akan Demokradiyya

'Yan sandan kasar ta Senegal sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa mutanen da suka amsa kiran jam'iyyun hamayya na yin Zanga-zanga.

 Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya ce a jiya juma'a ne mutane suka amsa kiran jam'iyyun hamayya domin yin gangamin yin kira da a gabatar da zabuka a bisa tsarin demokradiyya.

Tun gabanin haduwar mutanen, jami'an tsaro su ka taru a babban dandalin cibiyar mulkin kasar wato Dakar.Mutanen sun so yin zaman dirshen a babban dandalin birnin.

Daga cikin bukatun masu Zanga-zangar da akwai yin kiran ministan harkokin cikin gida da ya yi murabus. bayan da ya ce a zaben shugaban kasa da za a yi a shekara mai zuwa, za su tabbatar da cewa shugaba Macky Sall ya yi nasara.

Bugu da kari 'yan adawar sun yi kira da a kafa wata sabuwar hukumar zabe mai cin gashin kanta.

A ranar 24 ga watan Febrairu 2019 ne za a yi zaben shugaban kasa