Zaben Saliyo : Dan Takara Jam'iyya Mai Mulki Ne Ke Kan Gaba
Wani kwarya-kwarya sakamakon da hukumar zabe a Saliyo, ta fitar ya nuna cewa dan takara jam'iyya mai mulki ne a kasar, ke kan gaba a kidayar kuri'un da ake.
Shugaban hukumar zabe ta kasar (NEC), N'Ali Koroma ya bayyana a jiya Asabar cewa, dan takara Jam'iyyar (APC) mai mulki a kasar Samura Kamara ne ke kan gaba da kashi 44,6% .
Sakamakon ya kuma yi nuni da cewa, dan takara na babbar jam'iyyar adawa ta (SLPP) a kasar ne ke biye masa da kashi 42%, a yayin da dan takara na gungun jam'iyyun (NGC) a sahu na uku da kashi 6,6%.
Bayanai daga kasar dai sun nuna cewa akwai alamun za'a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasar, ganin yadda manyan jam'iyyun ke kud-da-duk a sakamakon.
Nan gaba ne ake sa ran hukumar zaben za ta bayyana sakamakon din dindin na zaben da aka kada kuri'arsa a ranar bakwai ga watan Maris din nan da muku ciki.