Kalubalen Da Ke Jiran Zababben Shugaban Kasa A Saliyo
(last modified Mon, 12 Mar 2018 05:25:46 GMT )
Mar 12, 2018 05:25 UTC
  • Kalubalen Da Ke Jiran Zababben Shugaban Kasa A Saliyo

Rahotonni suna bayyana cewa: Sakamakon zaben shugaban kasa na farko-farko a kasar Saliyo yana nuni da cewa: Babu dan takarar da zai samu yawan kuri'un da ake bukata wato fiye da kashi 55 cikin dari da hakan zai bashi damar lashe zabe lamarin da zai kai ga gudanar da zaben shugabancin kasar zagaye na biyu.

Hukumar zaben kasar Saliyo tana ci gaba da yin kira ga al'ummar kasar sun yi hakuri har a kai ga bayyana kashen sakamakon zaben shugabancin kasar musamman ganin yadda ga dukkan alamu babu dan takarar da zai samu yawan kuri'un da ake bukata na fiye da kashi 55 cikin dari domin samun nasarar lashe zaben shugabancin kasar.

A ranar Laraba 7 ga wannan wata na Maris ne al'ummar Saliyo da suka cika sharuddan zabe da yawansu ya kai fiye da miliyan uku suka gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan Majalisun Dokokin Kasar, inda yawan mutanen da suka tsaya takarar shugabancin kasar suka kai 16, duk da cewa 'yan takara da suke shahararru sune tsohon ministan harkokin wajen kasar Samura Kamara da ya fito daga jam'iyya mai mulki na kasar ta "All People's Congress" da kuma babban dan hamayyarsa Julius Maada Bio tsohon shugaban Majalisar Mulkin Soji na Kasar daga jam'iyyar Sierra Leone People's Party kuma sune suka samu yawan kuri'u a zaben ranar ta Laraba, sai dai babu wanda ya samu yawan kuri'un da ake bukata.

Tsohon shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma ya dauki aniyar sauka daga kan karagar shugabancin kasar bayan da wa'adin mulkinsa na biyu kuma na karshe ya kare tare da mika ragamar shugabancin kasar ga zababben shugaba da al'ummar Saliyo zasu zaba wa kansu lamarin da ke matsayin babban abin yabo musamman idan aka yi la'akari da yadda wasu shugabannin kasashen Afrika suke yin babakere a kan karagar mulkin kasashensu ta hanyar yin tazarce a kan karagar shugabancin kasar duk kuwa da cewa hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin kasashen.

Wannan zabe na shugabancin kasar Saliyo ya zo ne a daidai lokacin da kasar ke fama da tarin matsaloli musamman matsalar tattalin arziki da na zamantakewa, inda yawan rashin aikin yi ya haura zuwa kashi 70 cikin dari, baya ga bullar matsalar rashin kayayyakin kiwon lafiya da kuma uwa uba yin sama da fadi da dukiyar kasar. Sakamakon haka babban kalubalen da ke jiran duk wanda za a zaba a matsayin sabon shugaban kasa a Saliyo shi ne: Fuskantar tarin matsalolin da suke addabar al'ummar kasar a bangarori daban daban tare da kokarin ganin ya saukaka musu irin mummunan kangin rayuwa da suka shiga ciki.