Sudan Ta Kudu : An Sallami Ministan Kudi Da Wani Babban Jami'in Tsaro
Shugaba Salva Kiir, na Sudan ta Kudu, ya sallami ministan kudi na gwamnatinsa, Stephen Dhieu Dau, da kuma babban jami'in kula da horo da leken asiri na rundinar sojin kasar, Marial Chanoung.
A sanarwar da aka fitar da yammacin jiya a gidan talabijin din kasar, tuni aka maye gurbin Stephen Dhieu Dau da Salvatore Garang.
Sanarwar dai bata yi karin haske ba kan dalilin sallamar jami'an biyu ba.
Saidai labarin ya ce Mista Dau wanda ya rike mukamin ministan kudi na kasar tun daga 2016 ya dauki tsararen matakai don farfado da tallalin arzikin kasar da ya tabarbare.
Kasar Sudan ta Kudu mai arzikin man fetur, ta dogara ne dai da kashi 98% na kudin man fetur a kasafin kudin gwamnatinta, saidai ta fuskanci koma baya sakamakon rikicin da kasar ke fama dashi da kuma faduwar kudin man fetur a kasuwannin duniya.