Rikicin Kabilanci Ya Ci Rayukan Mutum 40 A Kwango
Akalla mutum 40 ne suka rasa rayukansu sanadiyar rikicin kabilanci a jamhoriyar demokaradiyar Kwango
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa daga kasar Kwango ya nakalto majiyar garin Bunia a wannan talata na cewa wani sabon rikicin kabilanci ya barke a wasu kauyuka na yankin Ituri na arewa maso gabashin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar salwantar rayukan mutane sama da 40.
Wani mai rike da sarautar gargajiya na yankin Ituri da ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana cewa an kai harin ba zata ne a kan mazauna kauyukan, kuma har yanzu ana ci gaba da bincike domin gano sauran gawawwakin da suka salwanta.
Sama da shekaru 20 kenanda yankunan tsakiya, gabashi, da kuma arewa maso gabashin jamhoriyar demokaradiyar Kwango ke fuskantar matsalar tsaro.
Kasawar jami'an tsaron kasar da kuma dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD da aka jibke a kasar ya sanya har yanzu an kasa dawo da tsaro gami da kwanciyar hankali a wadannan yankunan.