Kenya: Za A Kafa Wata Cibiyar Musulunci Domin Dakile Yaduwa Tsatsauran Ra’ayi
Musulmin kasar Kenya na shirin gina wata cibiyar musulunci wadda za ta mayar da hankali wajen fada da tsatsauran ra’ayin addini a kasar.
Shafin bc.co.uk ya habarta cewa, shugaban majalisar musulmin yankin Mombasa na kasar Kenya Abdulkadir Hidel ya bayyana cewa, za a kafa wata cibiyar musulunci da za ta yaki tsatsauran ra’ayi.
Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan cibiya za ta mayar da hankali ne ga ayyukan wayar da kai musamamn ga matasa, wadanda su ne aka fi saurin rudar su wajen wanke kwakwalensu da kuma saka su cikin kungiyoyin ta’addanci sakamakon cusa musu tsatsauran ra’ayi.
Kasar Kenya na daga cikin gabashin Afirka, kuma mafi yawan mutanen kasar mabiya addinin kirista ne, amma musulmi suna da rinjaye a yankin Mombasa.
Kungiyoyin 'yan ta'adda musamman masu alaka da kungiyar Alshabab suna kaddamar da hare-hare a cikin kasar Kenya lamarin da yake bakanta sunan adinin muslunci a kasar.