Dakarun Somaliya Sun Hallaka 'Yan Ta'addan Kungiyar Al-Shabab Su Bakwai
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29099-dakarun_somaliya_sun_hallaka_'yan_ta'addan_kungiyar_al_shabab_su_bakwai
Sojojin kasar Somaliya sun sami nasarar hallaka wasu 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Al-Shabab ta kasar su bakwai a wani hari da suka kai musu a garin bakin ruwan nan na Kismayo da ke kudancin kasar.
(last modified 2018-08-22T07:01:33+00:00 )
Mar 15, 2018 07:50 UTC
  • Dakarun Somaliya Sun Hallaka 'Yan Ta'addan Kungiyar Al-Shabab Su Bakwai

Sojojin kasar Somaliya sun sami nasarar hallaka wasu 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Al-Shabab ta kasar su bakwai a wani hari da suka kai musu a garin bakin ruwan nan na Kismayo da ke kudancin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Xianhua na kasar China ya jiyo kwamandan sojojin yankin Kismayon Mukhtar Abdi, a wata ganawa da yayi da manema labarai yana cewa sakamakon wasu bayanan sirrin da sojojin suka samu dangane da mabuyar 'yan ta'addan na Al-Shabab da kuma shige da ficensu, sun sami nasarar yi musu kwanton bauna inda suka hallaka bakwai daga cikinsu.

Kwamandan sojin ya kara da cewa sojojin sun kai wa 'yan ta'addan wannan harin ne a daidai lokacin da suke shirin kai wasu hare-haren ta'addanci a yankin.

Garin na Kismayo dai ya kasance mafi girman hanyar da 'yan ta'addan suke samun kudaden shigarsu tsawon lokacin da wajen ya kasance a hannunsu har zuwa lokacin da sojojin gwamnati suka kwace wajen daga hannunsu.