Rikici Gabanin Zaben Saliyo Zagaye Na Biyu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29209-rikici_gabanin_zaben_saliyo_zagaye_na_biyu
'Yan sanda da hukumar zabe a kasar Saliyo sun yi gargadi akan samun bullar tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa a wasu yankunan kasar.
(last modified 2018-08-22T07:01:35+00:00 )
Mar 19, 2018 03:38 UTC
  • Rikici Gabanin Zaben Saliyo Zagaye Na Biyu

'Yan sanda da hukumar zabe a kasar Saliyo sun yi gargadi akan samun bullar tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa a wasu yankunan kasar.

Bayannan da bangarorin suka fitar sun ce an samu rikice rikice a makon da ya shude tsakanin magoya bayan 'yan takara biyu da zasu fafata a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar.

Hukumar zaben kasar ta ce an samu barkewar rikici a yankunan Kono, Kailahun a gabashin kasar da kuma da Port Loko a arewacinn kasar, haka kuma an jikkata wani jami'in hukumar zabe a yankin Bo wanda yanzu haka yake jinya a asibiti.

Tuni dai jakadun kasashen Biritaniya, Jamus da Amurka da kuma kungiyar tarayya Turai suka bukaci ga bangarorin dasu kai zuciya nesa.

A ranar 27 ga watan Maris din nan ne za'a fafata a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Saliyo tsakanin dan takara adawa Julius Maada Bio, da kuma na jam'iyya mai mulki Samura Kamara.