'Yan Gudun Hijira 900,000 Sukayi Rejista A Habasha
Mar 19, 2018 03:44 UTC
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, ta ce sama da 'yan gudun hijira da masu neman mafaka 900,000 ne aka yi rajistansu a kasar Habasha.
Habasha dai ita ce wata kasa ta biyu dake karbar mafi yawan 'yan gudun hijira a Afrika, inda alkalumman da aka fitar suka nuna a karshen watan Fabariru 'yan gudun hijira da masu neman mafaka 909,301 ne akayi rejistansu.
Galibin dai mutanen sun fito ne daga kasashen Sudan ta Kudu, Somaliya, Eritrea, da Sudan da Yemen da kuma na wasu kasashen waje.
Saidai hukumar ta MDD, ta ce tana fuskanatar karancin kudin da take bukata na Dala miliyan 289 wajen taimakawa 'yan gudun hijira a Habasha a ayyukanta na 2018.
Tags