Najeriya: Shugaba Buhari ya fasa zuwa Rwanda
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29222-najeriya_shugaba_buhari_ya_fasa_zuwa_rwanda
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fasa zuwa kasar Rwanda domin halartar wani taron shugabanin Tarayyar Afrika kan yarjejeniyar kasuwanci.
(last modified 2019-01-16T04:00:45+00:00 )
Mar 19, 2018 15:28 UTC
  • Najeriya: Shugaba Buhari ya fasa zuwa Rwanda

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fasa zuwa kasar Rwanda domin halartar wani taron shugabanin Tarayyar Afrika kan yarjejeniyar kasuwanci.

A cikin sanarwar da ta fitar, ma'aikatar harakokin wajen Najeriya ta ce an soke tafiyar shugaban kasar  ne don samun isasshen lokacin da za a yi nazari  game da yarjejeniyar da kasashen Afrika suka amince da ita a watan Janairun 2012,yarjejeniyar ta shafi gudanar da kasuwanci ba tare da biyar  haraji ba a  tsakanin kasashen da suka sanya hannu.

A ranar Larabar da ta gabata ne majalisar zartawar kasar ta amince Najeriya ta shiga yarjejeniyar, to saidai fasawar da shugaba Buhari ya yi na zuwa kasar Rwanda ya sanya aka umarci wasu jami'an gwamnatin ta kasar da suka isa birnin kigali domin shirya zuwa na Buhari, dawowa kasar.

Kafin hakan dai,  kungiyar kwadago ta Najeriya ta yi gargadi game da amincewa da yarjejeniyar, inda ta ce matakin zai gurgunta masana'antu tare da haifar da rasa guraben ayyukan yi ga 'yan kasa.