Kasashen Afrika 44 Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Kasuwancin Bai Daya
Yau Laraba, kasashe 44 na kasashen Afrika sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kasuwancin bai daya tsakaninsu mai manufar samar da ci gaban tattalin arziki a nahiyar.
Kasashen dai sun cimma wannan yarjejeniya ce ta (ZLEC) a karshen taron shuwagannin kungiyar tarayya Afrika a birnin Kigali na kasar Ruwanda a cewar shugaban kwamitin gudanarwa na kungiyar ta (AU) Musa Faki.
Akwai dai kasashen da basu rattaba hannu kan yarjejeniyar ba, don a cewarsu suna bukatar lokaci don yin nazari, kuma zasu bayyana matsayinsu a yayin wani taron kungiyar a kasar Mauritania a watan Yuli na wannan shekara.
Kungiyar ta AU ta ce soke kudin kwastom tsakanin kasashen mambobin na (ZLEC) zai bada damar habaka wa da kashi 60% tattalin arzikin nahiyar nan da shekara 2022.
Za'a dai kwashe kawanaki 180 kafin dai a aiwatar da yarjejeniyar, sannan tana bukatar sanya hannu daga ko wacce kasa data sanya hannu kan yarjejeniyar.
Najeriya dai bata halarci taron ba, inda ta ce tana bukatar lokaci don nazari.