Gabon : An Sake Hana Jagoran 'Yan Adawa Fita Kasar Waje
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29322-gabon_an_sake_hana_jagoran_'yan_adawa_fita_kasar_waje
Jami'an tsaro a Gabon sun sake hana jagoran 'yan adawa na kasar, Jean Ping, fita daga kasar, a daidai lokacin da yake shirin hawa jirgi don zuwa birnin Paris na kasar Faransa.
(last modified 2018-08-22T07:01:36+00:00 )
Mar 23, 2018 01:21 UTC
  • Gabon : An Sake Hana Jagoran 'Yan Adawa Fita Kasar Waje

Jami'an tsaro a Gabon sun sake hana jagoran 'yan adawa na kasar, Jean Ping, fita daga kasar, a daidai lokacin da yake shirin hawa jirgi don zuwa birnin Paris na kasar Faransa.

Mista Ping, wanda tsohon shugaban kwamitin kungiyar tarayya Afrika ne, an hana shi fita daga kasar ta Gabon ne, saboda wani binciken shari'a wanda zai bada shaida.

Wasu majiyoyi sun ce, Jean Ping, zai bada shaida ne akan wani binciken shari'a da ake kan dan adawa nan Pascal Oyugu, da ake zargi da yiwa gwamnatin zagon kasa.

Wannan dai shi ne karo na uku a cikin wannan shekara da ake hana Mista Jean Ping, wanda shi ne ke jagorancin gungun jam'iyyun adawa na (CNR) a kasar ta Gabon, fita wata kasar waje, bayan an hana shi fita a ranakun 13 ga watan Janairu da kuma 3 ga watan Fabrairu da ya gabata.