An Shiga Rashin Tabbas Bayan Soke Zabe Zagaye Na Biyu A Saliyo
A Saliyo an shiga cikin rashin tabbas bayan da kotun kolin kasar ta soke zagaye na biyu na zaben shugabancin kasar.
A jiya Asabar ne dai kotun kolin kasar ta bukaci hukumar zaben kasar data dakatar da shirye shiryen zagaye na biyu na zaben.
Wannan matakin dai ya biyo bayan karar da jam'iyyar mai mulki ta shigar na zargin tafka magudi a zaben.
A cewar mai shari'a Ibarhim Sori Koroma na jam'iyya mai mulki ta APC (All Peoples' Congress), za'a gudanar da bincike kan zargin tafka magudi a zagaye na farkon kafin a je zagaye na biyu.
A ranar Litini ne ake sa ran kotun tsarin mulkin zata bayyana matsayinta kan zargin magudin a zaben zagayen farko, wanda dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta kasar SLPP (Sierra Leone people' party) cewa da Julius Maada Bio, ya lashe da 43,3% na yawan kuri'un da aka kada, a yayin da dan takara na jam'iyya mai mulki ta APC cewa da Samura Kamara ya samu kashi 42,7%, wanda ya basu damar zuwa zagaye na biyu.