An Fara Gudanar Da Zaben Shugabancin Kasa A Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29384-an_fara_gudanar_da_zaben_shugabancin_kasa_a_masar
An bude rumfunar zabe a larduna 27 da suke kasar Masar a safiyar yau Litinin domin fara gudanar da zaben shugaban kasa.
(last modified 2018-08-22T11:31:36+00:00 )
Mar 26, 2018 12:36 UTC
  • An Fara Gudanar Da Zaben Shugabancin Kasa A Masar

An bude rumfunar zabe a larduna 27 da suke kasar Masar a safiyar yau Litinin domin fara gudanar da zaben shugaban kasa.

Mahukuntan Masar sun sanar da cewa da misalin karfe 9 na safiyar yau Litinin an bude rumfunar zabe a lardunan kasar 27 domin fara gudanar da zaben shugaban kasa, inda gudanar da zaben zata kai har zuwa ranar Laraba.

Shugaban kasar Abdul-Fatah Al-Sisi yana daga cikin mutanen da suka fara fitowa domin kada kuri'arsu bayan sanar da bude rumfunar zaben a yau Litinin.

Shugaban hukumar zaben kasar ta Masar Lashin Ibrahim ya bayyana cewa: Al'ummar Masar zasu kada kuri'arsu ne a rumfunan zabe 13,687 da aka ware a duk fadin kasar da zasu kasance karkashin sanya - idon alkalai 18,678, kuma za a fara kidayen kuri'un ne a ranar karshe na zabe.