An Samu Raguwar Yaduwar Cutar Lassa A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29400-an_samu_raguwar_yaduwar_cutar_lassa_a_najeriya
Hukumar lafiya ta duniya ta ce an fara samun raguwar yaduwar cutar zazzabin Lassa a Najeriya.
(last modified 2018-08-22T07:01:36+00:00 )
Mar 27, 2018 01:19 UTC
  • An Samu Raguwar Yaduwar Cutar Lassa A Najeriya

Hukumar lafiya ta duniya ta ce an fara samun raguwar yaduwar cutar zazzabin Lassa a Najeriya.

A rahoton data fitar hukumar ta WHO, ta ce bayan tabbatar da mutane 400 sun kamu da zazzabin na Lassa yayin da wasu 100 suka mutu sanadin ta, a yanzu an fara samun raguwar yaduwarta, sai dai har yanzu da sauran rina a kaba.

Kididdiga daga hukumar WHO da cibiyar takaita yaduwar cutuka ta Nijeriya NCDC, sun nuna cewa, adadin sabbin masu kamuwa da cutar da wadanda ake hasashen sun kamu da ita ya ragu cikin makwanni biyar a jere.

Hukumar NCDC ta ce, a bana gwaje-gwaje da aka yi sun tabbatar da mutane 394 sun kamu da cutar, inda mutane 18 ne suka kamu da ita cikin makon da ya gabata, adadin da ya ragu idan aka kwatanta da mutane 54 da aka samu a watan da ya gabata.

Reshen hukumar ta WHO a Nijeriya, ya ce, akwai bukatar a ci gaba da sanya ido da gudanar da ayyukan tunkarar cutar, don tabbatar da ci gaba da cudanya da al'ummomi da nufin taimakawa wajen kare ci gaba da yaduwarta.