Saliyo : An Tsaida Ranar Zaben Shugaban Kasa Zagaye Na Biyu
Hukumar zabe ta kasa a Saliyo, ta tsaida ranar 31 ga watan Maris a matsayin ranar kada kuri'a a zaben shugaban kasar zagaye na biyu.
Wannan dai na zuwa ne bayan da kotun kolin kasar ta yi watsi da karar da wani jigo a jam'iyya mai mulki ya shigar na a dage zaben da aka shirya yi a yau Talata 27 ga wata, bisa zargin tafka magudi a zagaye na farko na zaben.
A saboda haka ne hukumar zaben kasar ta bukaci karin 'yan kwanaki don shirya zaben, inda ta tsaida ranar Asabar mai zuwa, ranar da za'a gudanar da zaben zagaye na biyu.
Kafin hakan dai an shiga cikin rashin tabbas bayan da kotun kolin kasar ta soke zagaye na biyu na zaben shugabancin kasar, inda za'a fafata tsakanin dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta kasar SLPP (Sierra Leone people' party) cewa da Julius Maada Bio, wanda ya lashe da 43,3% na yawan kuri'un da aka kada, a zagayen farko, da kuma dan takara na jam'iyya mai mulki ta APC cewa da Samura Kamara wanda ya samu kashi 42,7%.
Kimanin 'yan Saliyo miliyan uku da dubu dari daya ne da suka cancanci zabe ne zasu kada kuri'a a zaben zagaye na biyu a ranar Asabar idan Allah ya kai.