Jami'an Tsaron Kenya Sun Kame Wani Madugun 'Yan Adawa
(last modified Tue, 27 Mar 2018 17:16:50 GMT )
Mar 27, 2018 17:16 UTC
  • Jami'an Tsaron Kenya Sun Kame Wani Madugun 'Yan Adawa

Rahotanni daga Kenya sun ce jami'an tsaron kasar sun cafke deaya daga cikin jagororin 'yan adawar siyasa na kasar Miguna Miguna.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya habarta cewa, majiyoyin 'yan adawa a kasar ta Kenya sun tabbatar da kame Miguna Miguna, wanda dan kasar Kenya ne da yake dauke da takardun izinin zama dan kasa a kasar Canada.

A cikin watan da ya gabata ne jami'an tsaron kasar Kenya suka kame Miguna a yayin gudanar da wata zanga-zangar adawa da gwamnati, kuma aka fitar da shi daga kasar zuwa Canada, amma a cikin makon da ya gabata wata kotun kasar Kenya ta fitar da hukuncin da ya ba shi dama domin dawowa Kenya.

Rahoton ya ce a jiya ne Miguna ya iso Kenya, kuma ba tare da wani bata lokaci ba jami'an tsaro suka sake cafke da nufin sake tasa keyarsa zuwa kasar Canada.