Burkina Faso: Fiye Da Mutane Dubu Biyar Sun Zama 'Yan Gudun Hijira
(last modified Wed, 28 Mar 2018 09:27:17 GMT )
Mar 28, 2018 09:27 UTC
  • Burkina Faso: Fiye Da Mutane Dubu Biyar Sun Zama 'Yan Gudun Hijira

Kungiyar Agaji ta Red cross ta ce mutanen da ke yankin arewacin kasar ta Burkina Faso sun yi hijira ne domin kaucewa hare-haren masu akidar "takfiriyyah'

Kungiyar ta ci gaba da cewa; Tun daga watan Janairu na 2018 zuwa yanzu, iyalai 800 da suka kunshi mutane 5000 sun fice daga gundumar Soum mai iyaka da kasar Mali, inda su ka nufi kudancin kasar.

Arewacin kasar Burkina Faso mai iyaka da kasashen Mali da Nijar yana fuskantar hare-haren ta'addanci daga kungiyoyin masu wuce gona da iri a addini. A cikin shekaru uku mutane 133 ne aka kashe a hare-hare 80 da aka kai wa yankin.

Kungiyar ta Red Cross ta kuma kara da cewa; Daga 2017 zuwa yanzu, ta ba da taimako ga mutane fiye da 18,000 a cikin gundumar ta Soum.