'Yan Majalisar Zambiya Sun Jinkirta Kada Kuri'ar Tsige Shugaban Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29436-'yan_majalisar_zambiya_sun_jinkirta_kada_kuri'ar_tsige_shugaban_kasar
'Yan majalisar kasar Zambiya sun jinkirta tattaunawar da kuma kada kuri'ar da aka shirya za a gudanar a yau din nan Laraba kan daftarin kudurin da aka gabatar na tsige shugaban kasar Edgar Lungu bisa zargin yin karen tsaye ga kundin tsarin mulkin kasar.
(last modified 2018-08-22T07:01:37+00:00 )
Mar 28, 2018 11:41 UTC
  • 'Yan Majalisar Zambiya Sun Jinkirta Kada Kuri'ar Tsige Shugaban Kasar

'Yan majalisar kasar Zambiya sun jinkirta tattaunawar da kuma kada kuri'ar da aka shirya za a gudanar a yau din nan Laraba kan daftarin kudurin da aka gabatar na tsige shugaban kasar Edgar Lungu bisa zargin yin karen tsaye ga kundin tsarin mulkin kasar.

A makon da ya wuce ne jam'iyyar adawa ta  United Party for National Development (UPND), ta gabatar da daftarin kudurin tsige shugaba Lungu din da ta so a tattauna kansa a yau din nan Laraba, to sa dai magatakardar majalisar, cikin wata wasika da ya aike wa shugaban 'yan adawa a majalisar, Garry Nkombo, ya bayyana masa cewa saboda girman abin da za a tattauna din don haka akwai bukatar a yi dubi cikin lamarin sosai kafin a fara aiwatar da shi, yana  mai cewa a nan gaba za a sanar da su lokacin da za  a tattauna kan lamarin, wanda ake ganin kamar zai kai watan Yuni mai zuwa.

'Yan adawan dai suna cewa ne shugaba Edgar Lungu din ya karya kundin tsarin mulkin kasar ne a shekara ta 2016 bayan da ya ki mika mulki ga kakakin majalisar kasar a lokacin da 'yan adawan suka kalubalanci sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi suna masu zargin an tafka magudi, lamarin da shugaban ya yi watsi da shi.

Daga baya dai kotun ta yi watsi da karar da 'yan adawan suka shigar bayan da lauyansu ya gagara gabatar da hujjojinsa a wa'adin da doka ta tanadar.