An Kashe 'Yar Majalisar Dokokin Kasar Somaliya
Wasu 'yan bindiga sun bindige wata 'yar Majalisar dokokin kasar Somaliya a Magadushu babbar birnin kasar
Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta a jiya laraba wasu 'yan bindiga da ba a gano ko su waye ba sun bindige Ruqiya Abshir Noor daya daga 'yar majalisar dokokin kasar Somaliya a Magadushu babban birnin kasar.
Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya ko gungu da ya dauki alhakin wannan ta'addanci, to saidai Al'ummar kasar na zargin kungiyar ta'addancin nan ta ashabab mai alaka kut da kut da Alka'ida da kai hari, saboda ta rantse na ganin bayan jami'an kasar daya ba daya.
A cikin shekarun baya-bayan nan kasar ta Somaliya da ma kasar Kenya mai makwabtaka da ita suna fuskantar hare-haren ta'addanci na kungiyar Ashabab.
Ko baya ga matsalar ta'addanci kasar ta Somaliya na fuskantar matsalar yunwa sanadiyar karamcin abinci da take fama da shi sakamakon fari da kasar ta fuskanta a cikin shekarun baya-bayan nan.