Kenya : An Ci Tarar Wasu Manyan Jami'an Gwamnati Saboda walakanta Kotu
(last modified Thu, 29 Mar 2018 16:25:53 GMT )
Mar 29, 2018 16:25 UTC
  • Kenya :  An Ci Tarar Wasu Manyan Jami'an Gwamnati Saboda walakanta Kotu

Wani alkalin kotu a Kenya, ya ci tarar wasu manyan jami'an gwamnatin kasar tarar dala 2,000 saboda yin katsin landa a harkokin shari'a.

Alkalin ya bukaci manyan jami'an da suka hada da ministan cikin gida na kasar, da shugaban 'yan sanda da kuma shugaban hukumar shige da fice ta kasar, saboda shishigi a cikin harkar fitar da wani dan adawan kasar mai suna Miguna Miguna.

Jami'an uku duk sun ki amunce bayyana gaban babbar kotun kasar, don haka alkalin kotun, George Udunga, ya yanke masu hukuncin tara ta dalar Amurka 2,000 ga jami'an, kuma za'a cire kudin a cikin albashinsu na wata mai zuwa a cewar alkalin.

 Shi dai dan adawa Miguna, ya shaida cewa an muzguna mashi sosai ta hanyar duka da kuma bashi kwaya a filin jirgin saman da ake tsare dashi, kafin a cilasta masa ficewa daga kasar a karo na biyu.