Osinbajo: Ba Za Mu Yi Shiru Kan Ta'annutin Gwamnatin Jonathan Ba
Mataimakin shugaban kasar Nijeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewar ba za su yi shiru dangane da irin ta'annutin da gwamnatin Jonathan ta aikata ga tattalin arzikin Nijeriya din ba, yana mai cewa wajibi ne a ci gaba da sanar da 'yan Nijeriyan irin satar dukiyar kasa da aka yi a wancan lokacin wanda shi ne dalilin da ya sanya mutane cikin kuncin da suke ciki a halin yanzu.
Farfesa Yemi Osinbajon ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi wajen bikin cika shekaru 66 na daya daga cikin kusoshin jam'iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu da aka gudanar a Lagos, inda yayin da yake mayar da martani ga masu kiran gwamnatin da ta yi shiru kan irin badakalar da aka tafka a yayin gwamnatin da ta shude din ta ba da himma kawai wajen ci gaban kasar ya ce, inda yace ko shakka babu ba za su yi shiru kan irin barnar da aka yi a baya ba.
Mataimakin shugaban Nijeriyan ya kara da cewa manufar su ta ci gaba da magana kan ta'annutin da tsohuwar gwamnatin ta yi wa dukiyar kasa ita ce tabbatar wa 'yan kasar cewa lamurra ba za su ci gaba da tafiya haka ba, sannan bai kamata mutane su bari wasu 'yan tsirarru su ci gaba da sace dukiyar kasa ba, yana mai sake jaddada aniyar gwamnatin Nijeriyan ta hukunta duk wadanda aka same su da laifin satar dukiyar gwamnati.
Tun farkon hawarta karagar mulki, gwamnatin Muhammadu Buhari ta Nijeriyar take zargin gwamnatin PDP musamman shekaru biyar na tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan da yin watandar dukiyar gwamnatin kasar lamarin da ya sanya tattalin arzikin kasar cikin mawuyacin halin da yake ciki a halin yanzu, lamarin da ya sanya a ranar Litinin din da ta gabata shugaban jam'iyyar ta PDP, Uche Secondus, neman afuwar 'yan Nijeriyan saboda abin da ya kira kura-kuran da suka tabka yayin mulki, lamarin da ya jam'iyyar APC mai mulkin ta yi watsi da shi da kuma kiran 'yan kasar da kada su gafarta mata.