Sudan Ta Kudu Za Ta Rage Kungiyoyin Agaji Na Ketare
-
Tambarin kungiyar save the children
Wannan matakin dai na zuwa ne a daidai lokacin da milyoiyin al'ummar kasar ke fuskantar barazana yunwa.
Majalisar dokokin Sudan ta kudu ta amunce da wata doka ta rage yawan kungiyoyin agajin na kasashen waje dake aiki a kasar, duk kuwa da barazanar da milyoyin al'ummar kasar ke fuskanta na yunwa saboda yakin daya daidaita kasar.
Dokar data shafi kungiyoyin agaji na ketare da 'yan majalisun suka amunce da ita jiya Laraba, ta tanadi cewa kashi 20% ne kawai na ma'aikatan kungiyoyin 'yan kasashen waje zasu yi aiki a kasar, yayin da kashi 80% cilas su zama 'yan kasar ne.
Saidai dokar bata shafi kungiyoyin agaji ba na MDD irin su hukumar kula da 'yan gudun hijira (HCR) da hukumar abinci ta duniya (PAM) da kungiyar agaji ta kasa da kasa (CICR) ba.
Aman daga cikin kungiyoyi 140 da dokar ta shafa har da kungiyar likitoci ta kasa da kasa (MSF) da Oxfem da kuma Save the Children.
Tuni dai wasu kungiyoyin agaji suka nuna damuwar su akan wannan doka da zata saka milyoyin 'yan gudun hijira kasar cikin halin kaka-ni-kayi.