Najeriya: An Kai Harin Kunar Bakin Wake A Maiduguri
Mar 31, 2018 02:21 UTC
Rahotanni daga Najeriya na cewa a daren jiya Juma'a an kai harin kunar bakin wake a yankin Guna Garaj da ke birnin Maiduguri fadar mulkin jahar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.
Rahotannin sun tabbatar da cewa an kai harin ne a daren jiya da misalin karfe tara da rabi, amma babu wanda ya rasa ransa, sai dai dukkanin maharan uku sun halaka, yayin da wasu mutane da wurin suka samu raunuka.
Kafin lokacin dai an ji karar harbe-harben bindiga da igwa-igwa, amma babu wani bayani kan abin da ya faru.
Dangane da kai harin kunar bakin waken kuwa, babu wata kungiya ko gungun jama'a da suka dauki alhakin kai harin, amma tuni aka zargi kungiyar Boko Haram da hannu a harin.
Tags