Saliyo : Ana Zaben Shugaban Kasa A Zagaye Na Biyu
Mar 31, 2018 06:06 UTC
A kasar Saliyo kimanin mutane milyan uku da dubu dari ne da suka cancanci kada kuri'a ke kada kuri'a a zaben shugaban kasar a zagaye na biyu.
Ana dai fafata wa a zaben ne tsakanin dan takara Samura Kamara dake samun goyan bayan shugaba mai barin gado, a karkashin inuwar jam'aiyyar (APC) mai mulki, da kuma dan takara na babbar jam'iyyar adawa ta kasar (SLPP), Julius Maada Bio.
Rahotanni daga kasar dai na zuwa bayan bude runfunan zabe da misalin karfe bakwai na safe agogon wurin, ba'a samu fitowar jama'a ba sosai, kamar a zagayen farko a wasu mazabu a Freetown babban birnin kasar.
Da misalin karsfe biyar na yamma ne ogogo na GMT ne ake sa ran rufe mazabun.
Tags