An Kame Sama Da Mutane Dubu A Habasha
'Yan sanda a kasar Ethiopia sun kame sama da mutane dubu kan zarkin taka dokar ta bace a kasar
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto kafafen yada labarai na gwamnatin kasar ethiopia na cewa daga lokacin da aka sanya dokar ta bace a ranar 16 ga watan Favrayu zuwa yanzu, an kama mutane dubu daya da 107 saboda karya wannan doka.
Majiyar gwamnatin Ethiopian ta ce an kame wadannan mutane kan zarkin kai hari kan fararen hula da dakarun tsaro, da kuma sanya wuta a gidajen mutane da cibiyoyin kudi gami da kai farmaki kan ma'aikun gwamnati tare da tare hanyoyin al'umma.
Tun a ranar 16 ga watan Favrayu da ya gabata ce, aka sanya dokar ta bace a kasar ta Ethipia, biyo bayan murabus din da Piraministan kasar mista Hailemariam Desalegn ya yi daga kan mikaminsa.
A ranar juma'a 2 ga watan Maris, Majalisar dokokin kasar Habashar ta tsawaita dokar tabace har zuwa watani shida domin dakile zanga-zangar da ake yi a kasar
Bayan shekaru biyu na kin jinin gwamnati da kuma yawan sabanin dake cikin jam'iyarsa, Hailemariam Desalegn ya yi murabus daga kan mukaminsa.