Alaka Na Kara Tsami Tsakanin Sudan Da Saudiya
(last modified Sat, 31 Mar 2018 19:11:55 GMT )
Mar 31, 2018 19:11 UTC
  • Alaka Na Kara Tsami Tsakanin Sudan Da Saudiya

A cikin 'yan kwanakin nan ana ci gaba da samun sabani tsakanin mahukuntan biranan Khartoum da Riyad, bayan da sudan ta fidda rai kan taimakon da saudiya ta yi alkawarin bata, lamarin da ya sanda take kusantar kasashen Qatar da Turkiya

Cikin wani rahoto da ta fitar a wannan asabar, jaridar Al-Ikhbariya ta ce ganin yadda shugaba Al-Bashir na kasar sudan ya fida rai kan irin alkawarukan taimako da hukumomin saudiya suka yi masa, a cikin 'yan kwanakin ya shagaltu da kyautata alakar dipulomasiya tsakanin kasarsa da kasashen Turkiya da Qatar da suke rikici da kasar Suadiyan.

Jaridar ta ce duk da irin yanayi na matsin tattalin arziki da kasar Sudan din ke ciki a yanzu, to amma aminan nata kamar saudiya da hadaddiyar daular larabawa babu wani taimako na a zo a gani da suka yi mata.

A game da yarjejjeniyar da suka cimma na taimakawa kasar wajen gida madatsar ruwa da kuma sanya hanun jari a kasar ta Sudan, har yanzu mahukuntar birnin Riyad ba su cika wannan alkawari ba, bugo da kari, sai su kori duban ma'aikatan sudan din dake aiki a saudiya zuwa kasar su.

Tun daga watan Maris 2015,lokacin da saudiya ta fara kai harin wuce gona da irin kan al'ummar kasar Yemen zuwa yanzu, kasar Sudan ta aike da sojoji dubu hudu zuwa kasar ta yemen domin taimakawa saudiya a ta'addancin da take aiwatarwa a kasar.