'Yan Adawa Sun Zargi Jami'an Tsaro Da Hana Mutane Fitowa Zaben Saliyo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29532-'yan_adawa_sun_zargi_jami'an_tsaro_da_hana_mutane_fitowa_zaben_saliyo
A daidai lokacin da al'ummar Saliyo suke jiran sakamakon zaben shugaban kasar zagaye na biyu da aka gudanar a jiya asabar, dan takarar jam'iyyar adawa ta kasar ta Sierra Leone Peoples Party (SLPP), Julius Maada Bio ya dora alhakin rashin fitowar al'umma da aka fuskanta a kan yadda jami'an tsaro suka mamaye wajajen kada kuri'ar.
(last modified 2018-08-22T07:01:38+00:00 )
Apr 01, 2018 00:37 UTC
  • 'Yan Adawa Sun Zargi Jami'an Tsaro Da Hana Mutane Fitowa Zaben Saliyo

A daidai lokacin da al'ummar Saliyo suke jiran sakamakon zaben shugaban kasar zagaye na biyu da aka gudanar a jiya asabar, dan takarar jam'iyyar adawa ta kasar ta Sierra Leone Peoples Party (SLPP), Julius Maada Bio ya dora alhakin rashin fitowar al'umma da aka fuskanta a kan yadda jami'an tsaro suka mamaye wajajen kada kuri'ar.

Kafar watsa labaran Africanews ta ce Mr. Julius Maada Bio, ya bayyana hakan ne a yayin da yake magana dangane da rahotannin da suke cewa an sami karancin fitowar al'umma yayin zaben na jiya idan aka kwatanta da zagayen farko na zaben inda ya ce hakan ya samo asali ne sakamakon irin matakan tsaron da aka dauka da yadda jami'an tsaro suka fito da yawan gaske a mazabun zaben.

Rahotanni dai sun ce an samu karancin fitowar mutane a zaben na jiya, ta yadda wasu ma da kafar su suke takawa zuwa wajaje masu nisa don kada kuri'ar tasu sakamako haramta fitowa da motoci da jami'an tsaro suka yi wanda suka ce sun yi hakan ne don tabbatar da tsaron masu kada kuri'ar.

A jiya Asabar din ne dai al’ummar kasar Saliyon suka kada kuri’a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka fafata tsakanin dan takarar Jam’iyya mai mulkin kasar APC Samura Kamara da kuma jagoran ‘yan adawa na SLPP Julius Maada Bio bayan tsaikon da aka samu sakamakon umurnin da wata kotu ta bayar na a dakatar da gudanar da zaben da aka tsara gudanarwa a ranar Talatar da ta gabata 27 ga watan Maris har sai an saurari karar da aka shigar.