Takkadamar Diflomatsiyya Tsakanain Cuba Da Zambiya
Apr 02, 2018 06:27 UTC
Gwamnatin Zambiya ta ce bata ji dadin yadda jakadan kasar Cuba a kasar ya halarci bikin kafa samuwar jam'iyyar adawar kasar ba, tare da kira ga mahukuntan kasar ta Cuba dasu kira jakadan nasu.
Mista Nelson Pages Vilas, jakadan na Cuba a Zambiya ya dai halarci bikin ne a ranar Asabar data gabata, inda har ma a cikin jawabinsa ya yi fatan nasara ga sabuwar jam'iyyar adawar ta Zambiya.
Wannan lamari dai bai yi wa mahukuntan Zambiya dadi ba.
Wannan daukan bangaranci na jakadan na Cuba a cewar mahukuntan Zambiya ya janyo tanarbarewar diflomatsiyya mai kyawo tsakanin kasashen biyu.
Tags