Najeriya : Boko Haram Ta Kashe Mutum 18 A Maiduguri
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29572-najeriya_boko_haram_ta_kashe_mutum_18_a_maiduguri
Rahotannin daga Najeriya na cewa mutane a kalla 18 ne suka rasa rayukansu kana wasu 84 suka jikkata a wani hari da ake kyautata zaton na mayakan boko haram ne.
(last modified 2018-08-22T07:01:38+00:00 )
Apr 02, 2018 06:27 UTC
  • Najeriya : Boko Haram Ta Kashe Mutum 18 A Maiduguri

Rahotannin daga Najeriya na cewa mutane a kalla 18 ne suka rasa rayukansu kana wasu 84 suka jikkata a wani hari da ake kyautata zaton na mayakan boko haram ne.

An dai kai harin ne da yammacin jiya a cewar hukumar kula da agajin gaggawa ta NEMA a yankin, wacce ta tabbatar da lamarin.

An dai kai harin ne a unguwannin ale Shuwa da Bale Kura dake kewayen birnin na Maiduguri, kamar yadda wani jami'an hukumar ta NEMA  mai suna Bello Dambatto ya tabbatar wa da kamfanin dilancin labaren AFP.

Jami'an ya ce galibin mutenen sun mutu ne a musayar wuta tsakanin sojoji da 'yan bindigan. 

Wasu bayannai na daban sun ce an kuma kashe wasu 'yan kunar bakin wake biyu a daidai lokacin da suke kokarin tarwatsa kansu a unguwar Alikaranti,.