Abdulfattah Sisi Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Masar
(last modified Mon, 02 Apr 2018 17:26:35 GMT )
Apr 02, 2018 17:26 UTC
  • Abdulfattah Sisi Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Masar

Shugaban kasar Masar da ke kan kagarar mulki Abdulfattah Al-sisi ya sake lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar.

A sanarwar da hukumar zaben kasar Masar ta bayar a yau, ta sanar da cewa ta kammala kidaya dukkanin kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar, kuma Abdulfattah al-sisi ne ya samu kashi 97 cikin dari na dukkanin kuriun, yayin da abokin karawar tasa Musa Mustafa Musa ya tashi da kashi uku cikin dari.

Tun kafin lokcin gudanar da zaben dai gwamnatin Masar ta kame duk wani wanda ya nemi tsayawa takara take ganin zai tasiri a zaben, haka nan kuma ta yi barazana ga wasu wanda ala tilas suka janye, ta yadda Abdulfattah Sisi ne kawai zai ci karensa babu babbaka a zaben, wanda kuma hakan ne ya ba shi damar lashe zaben.

Abdulfattah Sisi wanda shi ne tsohon babban hafsan hafsoshin sojin Masar a lokacin shugabancin Muhammad Morsi, ya yi amfani da karfin bindiga wajen hambarar da Morsi, inda ya dare kan kujerar shugabancin kasar.