Guinea: Jam'iyyar Adawa Ta Dakatar Da Zanga zanga
Apr 03, 2018 05:43 UTC
Shugaba Alpha Conde da jagoran 'yan adawa na kasar Cellu Dalein Diallo sun yi wata ganawa ta kud da kud inda suka tattauna kan rikicin siyasa na kasar.
Wannan ganawar dai na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan adawa na kasar ke ci gaba da zanga zangar neman sahihin sakamakon zaben kananan hukumomin da aka gudanar a kasar a 4 watan Fabrairu da ya gabata.
A yayin ganawar, babbar jam'iyyar adawa ta kasar UFDG ta sanar da dakatar da jerin zanga zangar da take yi don baiwa kwamitin da aka kafa kan korafe korafen damar yin aikinsa.
Tags