Shirin Kasar Zimbabwe Na Kokarin Karfafa Alakarta Da Kasar China
Shugaban kasar Zimbabwe ya jinjinawa kasar China kan irin goyon bayan da take bai wa Zimbabwe musamman a fuskar tattalin arziki da siyasa tare da bayyana aniyar kasarsa ta ci gaba da karfafa alaka da kasar ta China a bangarori da dama.
A ziyarar aikin da ya fara a kasar China da tawagar da ke rufa masa baya tun a farkon wannan mako: Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya samu gagarumar tarba daga shugaban kasar ta China Xi Jinping, inda shugabannin biyu suka jaddada muhimmanci bunkasa alaka a tsakanin kasashensu a bangarori da dama musamman ganin yadda suke da kyakkyawar alaka ta tsawon lokaci.
Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya bayyana bukatar kasarsa ta ganin ta kara habaka alaka a bangarori da dama da kasar China musamman a bangaren aikin noma, ma'adani, masana'antu da sauransu, yayin da anata bangaren kasar China ta bayyana aniyarta ta zuba hannun jari a Zimbabwe har na kudi dalar Amurka biliyan daya da miliyan 400 musamman a bangaren samar da hasken wutan lantarki a kasar ta Zimbabwe.
A fili yake cewa: Wannan ziyara da shugaban kasar Zimbabwe ya kai zuwa kasar China a wannan lokaci tana da gagarumar muhimmanci musamman ganin yadda kasashen biyu suke da dadaddiyar alaka a tsakaninsu saboda a lokacin da kasashen yammacin Turai suka kakaba tarin takunkumi kan kasar Zimbabwe a zamanin mulkin Robert Mugabe, kasar China ce kadai take gudanar da alaka da Zimbabwe tare da taimaka mata a harkar tattalin arziki da karfin soji, kamar yadda wannan mataki da shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya dauka na kai ziyara zuwa kasar ta China zai kara karfafa alakar jakadanci da ke tsakanin kasashen biyu tare da karfafa mahukuntan China a kan ci gaba da goyon bayan Zimbabwe musamman a fagen siyasa.
Jean-Joseph Boillo manazarci kan harkokin alakar da ke tsakanin kasar China da kasashen Nahiyar Afrika yana da ra'ayin cewa: Kasar China tana kokarin ganin ta bunkasa alakarta da kasashen nahiyar Afrika musamman kasar Zimbabwe saboda kasancewar Zimbabwe mahada ce da take makobtaka da kasashen Afrika ta Kudu, Mozambique da Botswana da suke da tarin arzikin karkashin kasa. Kamar yadda ita ma kasar ta Zimbabwe take da bukatar ganin ta kara rayar da kyakkyawar alakar da ke tsakaninta da China musamman domin farfado da harkar tattalin arzikinta bayan tsawon shekaru tana fuskantar matsaloli a bangarori da dama sakamakon maida ita saniyar ware da aka yi.
Masharhanta suna da ra'ayin cewa: Duk da bukatar da mahukuntan Zimbabwe suke da ita na kyautata alakarsu da manyan kasashen duniya musamman kasashen yammacin Turai amma hakan ba zai hana su hanzarta janyo kasar China jiki ba a matsayinta na tsohuwar kawa da ta taimaka musu a lokacin tsanani tare da karfafa alakar da ke tsakaninsu a bangarori dama musamman a harkar tattalin arziki.