Sabon Shugaban Saliyo Ya Bukaci Hadin Kan 'Yan Adawan Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29674-sabon_shugaban_saliyo_ya_bukaci_hadin_kan_'yan_adawan_kasar
Sabon shugaban kasar Saliyo, Julius Maada Bio, ya kirayi abokin hamayyarsa a zaben shugaban kasar da ya sha kaye wato Samura Kamara da yayi watsi da batun kalubalantar sakamakon zaben da yace zai yi, ya zo a tafi da shi don ci gaban kasar, yana mai ishara da yiyuwar ba shi wani mukami a sabuwar gwamnatin.
(last modified 2018-08-22T07:01:39+00:00 )
Apr 06, 2018 05:10 UTC
  • Sabon Shugaban Saliyo Ya Bukaci Hadin Kan 'Yan Adawan Kasar

Sabon shugaban kasar Saliyo, Julius Maada Bio, ya kirayi abokin hamayyarsa a zaben shugaban kasar da ya sha kaye wato Samura Kamara da yayi watsi da batun kalubalantar sakamakon zaben da yace zai yi, ya zo a tafi da shi don ci gaban kasar, yana mai ishara da yiyuwar ba shi wani mukami a sabuwar gwamnatin.

Kamfanin dillancin labaran Reuters, ya ce shugaba Julius Maada Bio din ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da shi inda yace yana kiran Mr. Kamara din da yayi watsi da tafarki kalubalantar sakamakon zaben da yake yi, yana mai cewa lalle shi din nan yana da rawar da zai iya  takawa wajen ciyar da kasar Saliyo gaba.

Shi ma a nasa bangaren, Mr. Kamara ya shaida wa kamfanin dillancin labaran na Reuters yiyuwar yayi watsi da kalubalantar sakamakon zaben da yace zai yi sai dai kuma bai ce ko zai shiga cikin sabuwar gwamnatin ba.

Sakamakon zaben da hukumar zaben kasar Saliyo din NEC ta fitar na nuni da cewa  Julius Maada Bio dan takarar jam'iyyar adawa ta Sierra Leone People’s Party (SLPP) ya sami kashi 51.8 cikin dari na kuri'u miliyan 2.5 da aka kada a zaben da aka gudanar a ranar 31 ga watan Maris din da ya wuce, alhali abokin takarar na jam'iyyar All People’s Congress (APC) mai mulki  Samura Kamara, ya sami kashi 48.1 cikin dari na kuri'un da aka kada din.