Taron Gaggawa Na Kwamitin CEMAC
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29718-taron_gaggawa_na_kwamitin_cemac
A jiya Asabar ne kwamitin kula da manufofin kudi da bankuna na kasashen da ke tsakiyar Afrika (CEMAC) a takaice ya kammala wani taronsa na gaggawa a birnin N'djamena na kasar Chadi.
(last modified 2018-08-22T07:01:40+00:00 )
Apr 08, 2018 01:33 UTC
  • Taron Gaggawa Na Kwamitin CEMAC

A jiya Asabar ne kwamitin kula da manufofin kudi da bankuna na kasashen da ke tsakiyar Afrika (CEMAC) a takaice ya kammala wani taronsa na gaggawa a birnin N'djamena na kasar Chadi.

Shugaban kwamitin na CEMAC, Daniel Ona Ondo, ya bayyana cewa kasashen mambobin kwamitin na fuskantar matsaloli da suka hada da na tattalin arziki, tsaro, da kuma na tafitar da hukumomi.

Babbar manufar shirya taron shi ne tattauna hanyoyin shawo kan wadannan matsalolin dake zaman karfen kafa ga ci gaban kasashen da kuma tattalin arzikinsu.

Shekaru hudu kenan da kasashen wannan yankin na (CEMAC) su guda shida da suka da (Kamaru, Gabon, Equatorial Guinea, Jamhuriya Afrika ta tsakiya da kuma Chadi) ke fama da matsalar tabarbarewar tattalin arziki data kasafin kudi da kuma na ajiyar kudaden waje, sakamakon tarin basusuka.

Sai kuma koma baya ta fusktar ayukan kamfanoni da kuma rikice rikice na cikin gida.

A game da yadda wadannan matsalolin da tarnaki wa haddin kan jama' a a kasashen da kuma samun sauki wajen hada hadar kudaden bai daya na yankin ne, shuwagabbannin kasashen suka cimma wata matsaya a watan Disamba na 2016, wacce ta tanadi daukar matakan gaggawa na daidaito al'amuran da suka shafi tattalin arzikin kasashen yankin.

Girka tsarin tattalin arzikin wanda ya samu goyan bayan abokan hulda a fannin ci gaba da kudade da dabaru, ya taimaka sosai wajen farfado da harkokin kudi a yankin na CEMAC. 

Shugaban kwamitin Daniel Ona, ya ce tattalin arzikin kasashen yankin sun fuskanci koma baya ne, sakamakon matsalar tsaro dake shafar kasashen Kamaru,  Chadi da kuma Jamhuriya Afrika ta Tsakiya.

Mista Ondo, ya kara da cewa duk wadannan matsalolin suna da tasiri sosai kan sha'anin tattalin arzikin kasashen yankin.

Wannan ne ma yasa kuma, shuwagabannin kasashe mambobin kwamitin, suka dauki kwararen matakai a yayin taronsu da ya gabata a watan Oktoba na 2017, musamman kan samar da walwala ta fuskar shige da fice na jama'a da dukuyoyinsu.

Saidai duk wadannan matakan na bukatar taimaka wa jama'a don gannin matakan sun daure, inji Mista Ondo.