Kashe-kashe A Najeriya Laifin Gaddafi Ne – Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari, na Najeriya ya dora laifin kashe-kashen da ke faruwa a fadin kasar a kan tsohon shugaban Libiya, Mu’ammar Gaddafi.
Buhari wanda ke bayyana hakan a yayin ganawa da babban Bishop na Canterbury, Justin Welby a ranar Laraba, ya yi ikirarin cewa makaman da Gaddafi ya jibge wa magoya bayan sa ne aka rika yin safararsu a arewa ta tsakiyar kasar .
Matsalar dadddiya ce, a cewar shugaba Buhari, amma dai shigo da muggan makamai da kutsen da mahara suka rika yi daga yankin Sahel zuwa cikin kasashen Afrika ta yamma, don kuwa mun sha arangama da irinsu suna taya Boko Haram fada.
''Gaddafi ne ya rika bai wa wadannan mahara makamai kuma ya na yi masu tirenin na horaswa, bayan da aka kashe shi, sai suka rika tserewa da makaman da ke hannun su. .
“Makiyaya da aka sani ba su rike komai sai sandar kiwo da adda, amma an wayi gari su ne ke daukar muggan makamai.” Inji Buhari.
Ya kara yin watsi da zargin da wasu ke yi cewa kashe-kashen na da nasaba da addini ko kabilanci.