AU Ta Kira Manyan Kasashen Duniya Su Girmama Hurimin Siriya
Tarayyar Afrika AU, ta yi kira ga manyan kasashen duniya su hada hannu wajen warware yakin basasar kasar Siriya tare da girmama hurimin kasar.
Wata sanarwa da shugaban hukumar AU Moussa Faki Mahamat ya fitar, ta ce tana yin tir da duk wani amfani da makamai masu guba, amma ta bukaci a ba da muhimmanci ga hadin kan kasashen duniya wajen samar da mafita mai dorewa a siyasance, ga yakin basasar kasar saboda makomar al'ummar kasar kadai.
Sanarwar ta ce, nahiyar Afrika na sa ran mambobin kwamitin sulhu na MDD, musammam na din din din, za su ajiye banbancin dake tsakaninsu tare da yin dukkan mai yiwuwa wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya domin amfanin dukkanin bil'adama, wanda ya dace da nauyin da dokokin MDD suka dora musu.
Har ila yau, AU ta ce tana goyon bayan hadin kan kasa da kasa, kuma dole ne duk wani matakin da za a dauka, ya kasance bisa dogaro da kwararan shaidu da hukuma mai zaman kanta da adalci za ta gabatar, tare da kiyaye dokokin kasa da kasa.