Dubban 'Yan Gudun Hijira Suna Kwarara Daga Kasar Habasha
Apr 16, 2018 07:56 UTC
Fiye da mutane 700,000 ne su ka bar gidajensu daga yankunan da ake rikici akan iyakokin kasashen Habsha da Somaliya
Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ne ya ambato jami'an gwamnatin Habasha suna cewa; Rikicin da ake yi akan iyakokin kasashen biyu ya ci rayukan mutane da dama, tare da jikkata wasu.
Mazauna yankunan da ke kan iyakar su 710,000 suka fice daga gidajesu zuwa wuraren da za su tsira da rayukansu.
A watan Disamba na 2017 ma an yi rikici a yankin iyakokin kasashen biyu ya ci rayuka masu yawa da kuma jikkata wasu.
A cikin watannin bayan nan ma dai ana ci gaba da samun rikicin.
Tags