Fara Aiwatar Da Shirin Musayar Fursunoni Tsakanin Kasashen Zambiya Da Namibiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3004-fara_aiwatar_da_shirin_musayar_fursunoni_tsakanin_kasashen_zambiya_da_namibiya
An fara shirin aiwatar da Yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kasashen Zambiya da Namibiya kan musayar fursunoni.
(last modified 2018-08-22T06:58:02+00:00 )
Mar 27, 2016 04:53 UTC
  • Fara Aiwatar Da Shirin Musayar Fursunoni Tsakanin Kasashen Zambiya Da Namibiya

An fara shirin aiwatar da Yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kasashen Zambiya da Namibiya kan musayar fursunoni.

Shugaban hukumar kula da gidajen kurkuku a kasar Namibiya Raphael Tuhafeni Hamunyela ya bayyana cewa: Tun a shekara ta 2012 aka rattaba hannu kan yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin gwamnatocin kasashen Zambiya da Namibiya amma sai a wannan lokaci yarjejeniyar zata fara aiki.

Hamunyela ya kara da cewa: A halin yanzu haka kasarsa ta Namibiya tana da fursunoni biyu ne kacal a gidan kurkukun Zambiya, yayin da 'yan kasar ta Zambiya yawansu ya kai 89 a gidajen kurkukun Namibiya.