Najeriya : An Cafke Sanatan Da Ya Tura 'Yan Daba Sace Sandar Majalisa
Rahotanni daga Najeriya na cewa, 'yan sanda kasar sun cafke sanata Ovie Omo-Agege, wanda ake zarginsa da tura 'yan daba don sace sandar majalisar dattawa.
'Yan sanda sun kame sanatan ne a harabar majalisar dokokin kasar, inda suka sa shi a bakar mota suka yi gaba da shi.
Da safiyar yau ne wasu da majalisar ta yi zargin 'yan daba ne karkashin jagorancin Sanata Omo-Agege, wanda aka dakatar da shi a makon da ya wuce, suka kutsa zauren majalisar yayin da ake zama, suka 'sace' sandar.
Kafin cafke sanatan, majalisar ta bai wa Sfeto Janar na 'yan sanda da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS, umarnin su nemo sandar a cikin sa'O'I 24, sannan su kamo wadanda suka sace sandar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya fitar, ta bayyana wannan al'amari da cin amanar kasa.
Wasu bayanai na daban na cewa an kawo wata sandar ta wucin-gadi an ajiye.