Gwamnatin Kasar Zimbabwe Ta Kori Dubban Jami'an Jinya Daga Aikinsu.
(last modified Thu, 19 Apr 2018 06:22:57 GMT )
Apr 19, 2018 06:22 UTC
  • Gwamnatin Kasar Zimbabwe Ta Kori Dubban Jami'an Jinya Daga Aikinsu.

Gwamnatin kasar Zimbabwe ta bada sanarwar korar dubban jami'an jinyan kasar masu yajin aikin neman kasar albashi.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya nakalto mataimakin shugaban kasar ta Zimbabwe Mr Costantino Chiwenga yana bada wannan sanarwan a ranar Talatan da ta gabata, ya kuma kara da cewa gwamnatinsa ta dauki wannan matakin ne don kawo dauki ga marasa lafiya a manya manyan asbitocin kasar wadanda suke bukatar taimakon wadannan ma'aikata.

Costantino Chiwenga ya kara da cewa jami'an jinya sun shiga yajin aiki ne don nuna goyon baya ga wata jam'iyyar siyasa a kasar. Sannan ya kammala da cewa zai maye gurbinsu da jami'an jinya wadanda suka yi ritaya da kuma wadanda basa da aikin yi.

Makonni kadan bayan da likitoci suka kawo karshen yajin aikin da suka shiga a kasar ta Zimbabwe ne jami'an jinya ma suka shiga yajin aiki don neman karin albashi, wanda ya jefa marasa lafiya da dama cikin halin kakanikaye a manya manyan asbitocin kasar.