Sudan Ta Kai Karar Masar A Gaban Majalisar Dinkin Duniya
Ministan harkokin wajen kasar Sudan Ibrahim Ghandur ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kai karar Masar a gaban komitin tsaro na Majalisar dinkin duniya.
Kamfanin dillancin labaran Anatolia ya nakalto ministan yana fada a gaban majalisar dokokin kasar ta Sudan a jiya Laraba. Ya kuma kara da cewa Sudan ta gabatarwa komitin tsaro na Majalisar dinkin duniya takardun koke har guda uku kan kasar Masar.
Koke na farko inji ministan shi ne sauya kan iyaka a tsibiran Teeron da Sanafir a cikin watan Afrilun shekara ta 2016. Sai kuma na biyu, gwamnatin kasar ta Masar tana gina tashoshin jiragen ruwan kamun kifi a Shalateen da Aburamad a cikin watan Febrerun shekara ta 2017, sannan daga karshe Masar ta gudanar da zaben shugaban kasa a yankuna masu kama da kusuruwowi uku, wato Hala'ib da Shalateen da kuma Aburamad wadanda kasashen biyu suke takaddama a kan mallakarsu tun lokacin samun 'yancin kan kasar Sudan a shekara ta 1958.
Banda haka akwai sabani tsakanin kasashen Masar Sudan da kuma Ethiopia kan gina madatsar ruwa ta Annahda a kan kogin nilu a kasar Ethiopia.